Mohammed Buba Marwa: Shari’ar da ake da Abba Kyari ba zata dauki wani dogon lokaci ba.

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Muhammad Buba Marwa yace shari’ar da ake da tsohon mataimakin kwamishinan dan sanda, Abba Kyari ba zata dauki wani dogon lokaci a kotu ba.

Marwa wanda ya bayyana haka a wani shirin gidan talabijin na channels ranar juma’a, yace kama sauran jami’ai biyu da ake zargi da laifin ya nuna cewa za’a gaggauta hukunci kan lamarin.

“An riga an kama jami’ai biyu da ake zargi da laifin kuma an tura su kurkuku, kaga wannan yana nuni da cewa shari’ar Abba Kyari ba ata dau wani lokaci ba,”

Marwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.