Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kwatanta matakin da mai shari’a Tanko Muhammad ya dauka na barin mukaminsa na alkalin alkalan Najeriya a matsayin abin a yaba.
Atiku a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ta shafinsa na Facebook, ya yi fatan alheri ga mai shari’a Tanko kamar yadda ya yabawa tsohon Alkalin Alkalan kan wannan aiki da hidimar da ya yi wa kasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da yi wa sabon mukaddashin CJN da aka rantsar, Mai shari’a Olukayode Ariowoola fatan samun nasara yayin da ya tashi tsaye domin cike gibin.
Atiku ya tabbatar wa sabon mukaddashin CJN kan kudirin sa na ciyar da iyakokin shari’a ’yancin kai da kuma inganta bangaren raba madafun iko a matsayin ginshikin zurfafa dimokaradiyya da ci gaba.
Dazu gidan talabijin na Channels sun ruwaito cewa Mai shari’a Tanko ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Litinin din da ta gabata saboda wasu matsalolin rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Daga nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin babban jojin Najeriya (CJN).
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, shugaban ya ce za a tuna da mai shari’a mai barin gado saboda gudunmuwar da ya bayar ga bangaren shari’a a Najeriya, da karfafa dimokaradiyyar mu da ci gaban kasa.