Babban jojin Najeriya, Mai shari’a Tanko Muhammad, ya yi murabus, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito a ranar Litinin.
Majiyoyi sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa Mai Shari’a Muhammad ya yi murabus ne a daren Lahadin da ta gabata, saboda rashin lafiya a matsayin dalilin yanke hukuncin.
Har ila yau, bayanai sun nuna cewa ana ci gaba da shirye-shiryen rantsar da babban alkalin kotun kolin kasar mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya na riko.
Rahotanni sun ce nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwar a hukumance.