Mai Shari’a Olukayode Ariwoola zai zama sabon Alkalin Alkalai.

A yau za’a rantsar da Justice Olukayode Ariwoola a matsayin sabon Shugaban Alkalan Najeriya CJN biyo bayan murabus din CJN Tanko Mohammad daga babbar kujerar.

Mai magana da yawun Tanko Mohammed, Ahuraka Isah, ya tabbatar da murabus din maigidansa da safiyar Litinin. Leadership ta ruwaito cewa za’a rantsar da sabon Alkalin Alkalai misalin karfe 11 na safe.

Idan ta tabbata ya zama, Justice Olukayode Ariwoola zai rike mukamin har zuwa shekarar 2028’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *