Jami’an ‘yan sanda sun gano gawarwakin matasa 17 a gidan rawa.

Jami’an ‘yan sanda sun soma binciken a game da mutuwar wasu matasa da aka gano gawarwakinsu a wani gidan rawa da ke yankin kudancin Afirka ta Kudu.

Al’ummar Afrika ta Kudu sun wayi garin wannan Lahadin a cikin jimami bayan da aka gano gawarwakin wasu mutum akalla 17 a wani gidan rawa. Ba a kai ga gano musababbin mutuwar mutanen da akasarinsu matasa ne da shekarunsu ba su haura ashirin ba.

Gidan rawan na wani yanki mai suna East London da ke Kudancin kasar Afirka ta Kudu, kuma a cewar babban jami’in ‘yan sandan lardin Birgediya Thembinkosi Kinana, da wuya a iya fahimtar abin da ya janyo wannan mutuwar bakatatan amma ya nemi hadin kan jama’a wajen bayar da bayanan da za su iya taimakawa binciken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *