2023: Kwankwaso ya fi Peter Obi Gogewa A Harkar Siyasa Don Haka Ba Zai Iya Zama Mataimakin sa ba – Jibrin

Tsohon dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa Rabiu Kwankwaso zai iya zama abokin takarar Peter Obi.


Ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Television’s Sunday Politics a yayin da rahotanni ke cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na tattaunawa da Obi kan shirin hadewar.

A cewar sa:


“A zahiri, Kwankwaso ba zai iya zama abokin takarar Peter Obi ba. Bisa kowane ma’auni, Kwankwaso ne ya kamata ya zama dan takarar shugaban kasa,” in ji jigon a hiran.


“Kwankwaso ya fi shi gogewa a harkar siyasa. Kuma ya fi shi sanin yadda zai ci zabe”.


Ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ne kadai dan siyasa a yankin Arewacin Najeriya da ke da dimbin magoya baya kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya jaddada cewa baya ga Obi, jam’iyyar NNPP na duba wasu ‘yan takara.


“Muna aiki don samun abokin takarar shugaban kasa,” in ji shi, yana kira ga yankin kudu maso gabas da su goyi bayan NNPP. Jubrin ya ce jam’iyyun APC da PDP sun ci amanar yankin. Don haka, ya ce ya kamata yankin kudu maso gabas su yi wa NNPP goyon baya”.


“APC da PDP sun ci amanar Kudu maso Gabas sosai, haka kuma. Sun yi wa PDP aiki sosai. Amma jam’iyyun sun jefar da yankin kudu maso gabas, sun ce musu, ‘bama bukatar ku,” inji shi.


“A baya kudu maso gabas sun tattaunawa akan shugabancin kasar nan tun Ekwueme. Dama ta farko da suke da ita a yanzu ita ce ta Kwankwaso. Dole ne su yi tunani sosai don kada su zubar da kuri’unsu. Su zo suyi sbokin takara. Wannan ita ce mafi kyawun dama da sukeda shi”.


Jubrin ya kara da cewa:

“Ya kamata kudu maso gabas su yi tunani karara sannan su hada kai da Kwankwaso.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *