Ya bayyana cewa Mande na aiki ne a Hukumar Jin Dadin Alhazai lokacin da ya tsinci dalla 800 mallakar wata maniyaciyya, Hajiya Hadiza Usman.
“Yayin da ya ke aikinsa a sansanin mahajjata, PC Mande ya tsinci $800 a kasa ya kuma mayarwa Direkatan Hukumar Alhazai, Alhaji Sada Salisu Rumah. “PC Mande ya bayyana cewa tsoron Allah ne yasa ya mayarwa hukumar alhazai kudin domin a mayarwa mai shi.
“Salisu Rumah ya yaba wa dan sandan saboda halin gaskiya da amana,” ya kara da cewa. A cewar Isah, kwamishinan yan sanda ya ji dadin gaskiyar da Mande ya nuna ya kuma yi kira da sauran yan sanda su yi koyi da shi.