Da alamu rikicin cikin gidan da ya samu asali tun daga bayyana Sunan gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mutumin da zai dafawa Dan takarar jamiyyar PDP baya a zaben 2023 na neman daukan sabon salo biyo bayan yadda jiga-jigan jamiyyar daga shiyyar kudancin kasar nan suka kauracewa wata liyafa girmamawa da aka shiryawa Okowa a Asaba babban birnin jihar Delta.
Mashaahuran Yan jamiyyar da suka kauracewa liyafa sun hada da tsofaffin gwamnonin yankin da suka hada da James Ibori da Emmanuel Uduaghan
Da yake jawabi a yayin liyafar, Gwamna Ifeanyi Okowa ya yabawa alummar Jiha bisa goyon baya da kaunar da suka nuna masa, ya kuma yabawa Atiku Abubakar da shugabancin jamiyyar PDP ta kasa bisa amincewar dashi a matsayin Dan takarar mataimakin shugaban kasa.