Jami’ar Lincoln da ke Birtaniya ta dakatar da Sanata Ike Ekweremadu da cigaba da aiki a matsayin farfesa mai ziyara.

Jami’ar Lincoln ta hana tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu cigaba da aikinsa a matsayin farfesa mai kai ziyara bayan zarginsa da safarar yaro dan shekara 15 zuwa Birtaniya don cire kodarsa, rahoton Channels Television.

A halin yanzu, Mr Ekweremadu da matarsa, Beatrice suna tsare hannun hukuma a Birtaniyan kan zargin, suna jiran shari’a a ranar 7 ga watan Yuli.

Ekweremadu ya shafe kimanin makonni biyu a Birtaniya kafin aka kama shi, bayan ya gana da yan Najeriya mazauna Birtaniya a Lincoln kimanin kwanaki 10 da suka gabata. Ya kasance yana koyarwa a matsayin farfesa na ‘corporate and international linkages’ a Jami’ar Lincoln. Amma, a cewar mai magana da yawun jami’ar da ya yi magana da wata jarida ta Birtaniya, Daily Mail, Jami’ar ta ce ta dakatar da shi daga duk wani aiki a hukumance.

“Galibi, farfesa mai ziyara, tamkar irin wannan, ba zama ya ke a jami’ar ba, kuma ba a biyansa albashi kawai shawarwari ya ke bada wa,” a cewar kakakin jami’ar. “Mun damu matuka da yanayin zargin amma duba da cewa yan sanda ba su kammala bincike ba, ba za mu ce wani abu fiye da haka’.

“Yayin da ake bincike, mutumin ba zai cigaba da aiki a matsayin farfesa mai ziyara ba a Lincoln.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.