Jami’an yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar yan sandan Interpol sun yi nasarar kwato wasu motoccin da aka sace daga Najeriya a Nijar.

Jami’an yan sandan Najeriya da hadin gwiwar yan sandan kasa da kasa ta Interpol sun yi nasarar kwato wasu motocci da aka sace daga Najeriya a Jamhuriyar Nijar. Mai magana da yawun yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da hakan.

Ya ce:

“Sifeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya yaba wa hadin gwiwa tsakanin kasashe 194 na yan sanda masu yaki da laifuka na kasa da kasa wacce ta taimaka wurin yaki da laifuka a duniya.

“IGP din har wa yau ya yaba wa sashin binciken manyan laifuka, saboda amfani da bayanai da suka samu a hannun INTERPOL don dakile laifukan kasa da kasa musamman abin da ya shafi kasashen Afirka da muke makwabtaka da su.

“Ya yi wannan jawabin ne bayan nasarar kwato wasu motocci guda uku da aka sace daga Najeriya aka kai Jamhuriyar Nijar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *