Hukumar Hisbah Za Ta Kafa Sharruda Kan Kafofin Sada Zumunta.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a halin yanzu tana shirin yin dokar kafa sharruda kan amfani da kafafen sada zumunta wato soshiyal midiya. Domin hakan, hukumar tana hadin gwiwa da Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano (KSCB).

Ismail Na’abba Afakallah, Babban Direktan KSCB, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi.

Dandalin sada zumuntar na lalata tarbiyar yaran mu, Afakallah Ya ce hukumar ta sa za ta mayar da hankali ne sosai kan fim industry, soshiyal midiya, musamman TikTok, da ya bawa masu karfin fada a ji a dandalin sada zumunta aikata badala.

“Hukumar mu da Hisbah ta kafa kwamiti da zai samar da hanyoyin magance wannan matsalar. Ba jaruman Kannywood kadai ke aikata badala ba a Tik Tok, mafi yawancin masu badala da shi ba yan industry bane. “Kallubale da ta shafi duniya. Mutane na ganinsa cewa duniya ce kuma za su iya duk abin da suke so. Kuma ba za mu iya barin hakan ya bata tarbiyar yaran mu ba”

Ya bayyana damuwarsa kan cewa an kirkiri dandalin sada zumunta ne don nishadi da watsa bayanai masu amfani amma mutane suna amfani da shi ta hanyar da bai dace ba.

“Yanzu suna amfani da damar don yada bayanai marasa amfani. Za ka ga manyan mata suna tika rawa na rashin mutunci da wasu abubuwan rashin tarbiya, musamman a Tik Tok da Instagram.”

Ya yi kira ga iyaye su saka idanu kan abin da yayansu ke yi a soshiyal midiya don kada su lalace.

Leave a Reply

Your email address will not be published.