Atiku bai san Kwankwaso da Tinubu da kuma Obi ba ne a siyasa – cewar Dino Malaye.

Yayin da zaben shugabancin kasar nan na shekara 2023 ke kara kusantuwa, Tsohon Sanata Dino Malaye ya bayyana Dan takarar jamiyyar PDP Atiku Abubakar a matsayin gogaggen da siyasa da ke da rinjaye a kusan dukkanin jihohin kasar nan.


A wani jawabi da yayi a shafin sa na manhajar sadarwa zamani na Facebook, Dino Malaye ya bayyana Atiku a matsayin Dan siyasa daya tilo a kasar nan da ka iya samu kaso Ashirin da biyar cikin Dari na kuri”un masu zabe a dukkanin jihohin fadin Najeriya.


A don haka ya bayyana sauran Yan takara da suka hada da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da Obi na jamiyyar LP da kuma Ahmad Bola Tinubu na APC a matsayin Yan rakiya a zaben shekara ta 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *