Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya rawaito Buhari yana bayyana haka a cikin wata sanarwa mai taken‘Ba ji dadin Hare-haren Coci a ‘yan kwanakin nan ba
Buhari ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai wajen yin addu’a tare da rike wadanda abin ya shafa da iyalansu a cikin zukatansu da tunaninsu.
Ya ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda suka kai hare-haren a gaban kotu,ya kuma bukaci dukkan ‘yan Najeriya su sani cewa, duk wani mugu muguntarsa za ta dawo kansa ya daidaice.