Shugabar Kwamitin Harkokin Zabe na Majalisar Wakilai, Aisha Dukki, ce ta bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Larabar.
A baya dai hukumar ta sanya ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta rufe sabunta rajistar.
Sai dai kiraye-kirayen da ake mata na kara wa’adin bisa fitowar dafifi da ’yan Najeriya sukai domin mallakar rajistar ya sanya ta amsa kiran.
Yanzu haka dai bayan kwamitin zaben majalisar ya gana da Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, sun amince da kara wa’adin ya dara ranar 30 ga watan Yunin 2022 da majalisar ta bukata.
A hannu guda kuma shugabar ta ce duk da hukumar zaben ta amince da bukatar majalisar ta kara wa’adin, ba lallai ta kara yadda majalisar ta bukata ba, sai dai za su koma su tattauna mafita kafin sanar da wa’adin da za su iya karawa.
To sai dai wata majiya daga hukumar zaben ta bayyana cewa mawuyaci ne a iya kara wa’adin da zai dara 30 ga watan Yunin, kuma da yiwuwar hukumar ta daukaka kara kan dakatarwar da kotu tayi mata na rufe sabunta rajistar a ranar 30 ga watan Yunin.