Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta bukaci karin taimako daga kasashen duniya, a yayin da take kokarin shawo kan mawuyacin halin da ake ciki bayan afkuwar mummunar girgizar kasa a Kudu maso Gabashin kasar.

An yi amanna cewa akwai mutum fiye da 1,000 da suka mutu a lardin Paktika kadai wato wajen da lamarin ya faru, sannan kuma akwai wasu har da yanzu ke binne a cikin baraguzan ginin gidajensu da suka rushe.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan Ramiz Alakbarov, ya ja hankalin kasashen duniya da su kawowa kasar dauki.

A cewarsa akalla gidaje 2,000 ake hasashen sun rushe, saboda haka mutane da dama sun rasa matsugunnai.
Taliban ta ce ana matukar bukatar abinci da tantunan da za a ajiye daruruwan mutanen da suka rasa muhallansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *