Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce wajibi ne shugabannin Kananan Hukumomin Jihar su tashi tsaye wajen yaki da ’yan bindigar da suka addabi yankunansu, ba tare da jiran wani ba.


Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taro su tare da Kansilolinsu kan sha’anin tsaron Jihar.


Offishin mai bai wa Gwamna Shawara kan harkokin tsaro karkashin Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina ne ya shirya taron domin duba matsalar tsaron da ta addabi Jihar.


A cewar Masari, wajibi ne su fito su kare tare da ceto yankunan nasu ba tare zaman jiran sai an nemo su ko an kawo masu dauki daga wani waje ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *