Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a yau Laraba ta ce shugaban zai halarci buɗe bikin a hukumance ranar Juma’a.
Taron, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ƙungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ƙasa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka da Turai da kuma yankin Pacific.
Ministci da manyan jami’an gwamnatin Najeriya takwas ne za su yi wa Buhari rakiya zuwa Rwanda.
Ana sa ran shugaban zai dawo gida Najeriya ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni.