Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ya ki amfani da shawarar da Bankin ba da Lamuni na Duniya (IMF) da sauran masana tattalin arziki suka ba shi kan cire tallafin man fetur.


Shugaban kasar ya ce dole ta sanya kasashen Yamma suka fara fahimtar banbancin abin da yake a takarda da kuma na zahiri.


Da aka tambaye shi dalilin kin cire tallafin, Buhari ya ce, “Yawancin kasashen Yamma yanzu suna biyan tallafin man fetur Kuma babu dalilin da zai sa Nigeria ta cire nata.


A cewar Buhari da fari gwamnatinsa ta shirya cire tallafin gaba daya nan da karshen shekarar nan, sai dai bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma la’akari da abubuwan da ke faruwa, sun fahimci hakan ba Mai yiwu bane.


Yace abin da kasar nan ta fi bukata shi ne inganta yawan man da take hakowa da tareda tacewa. Yanzu haka kasar na hada gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu na Dangote da BUA da kuma Waltersmith wadanda suke kafa matatun man fetur.


Inda yayi albishir da cewa Da zarar an kammala kafa wadannan masana’antun na bangaren mai da kuma na samar da abinci, matsalar hauhawar farashin kayayyaki za ta kau a Najeriya.


A baya dai IMF da Bankin Duniya da masana tattalin arziki da dama sun sha ba Shugaban shawarar janye tallafin gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *