Majalisar Likiitoci ta Najeriya ta (MDCN) tace ba za ta yarda da duk wata shaidar karatu kan likitanci da ɗalibai suka samu daga jami’o’in kasar Ukraine ba a shekarar nan ta 2022.

Majalisar wadda ke sa ido kan harkokin lafiya a kasar nan ta ce an ɗauki matakin ne saboda yaƙin da ake yi a ƙasar sakamakon hare-haren da Rasha ke kaiwa, abin da ya sa aka rufe azuzuwan jami’o’i da manyan makarantun ƙasar.


Wata sanarwa da majalisar ta fitar a shafinta na Twitter ta bayyana cewa tana sanar da jama’a cewa majalisar likitocin ba za ta yarda da shaidar karatun digiri ba kan harkokin lafiya da aka samo daga Ukraine a 2022 har sai harkokin karatu sun koma yadda aka saba.


Da yawa daga cikin jami’o’in kasar dai na ci gaba da karatu ta intanet, matakin da majalisar likitocin ta ce ya saɓa wa manhajar koyar da aikin likitanci.


A cewar sanarwa duk wani horon likitanci da aka samu ta intanet ba mai karɓuwa ba ne kuma ba za ta amince da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.