Majalisar Dattawan kasar nan ta ce an gano mabuyar yan ta’adda a kananan hukumomi uku a jihohin Kwara da Niger.

Wannan na cikin batutuwan da aka tattauna a majalisar bayan wani sanata ya gabatar da kudiri kan tabarbarewar tsaro a Kainji Lake National Parki da garuruwa da ke kananan hukumomin Kaima, Baruten da Borgu a Jihar Niger.


A cewar wanda ya gabatar da kudirin, Sanata Sadiq Umar, garkuwa da mutane da sauran laifuka sun zama ruwan dare a garuruwan da ke kusa da Kainji Lake National Park kuma hakan ya saka tsoro a zukatan mutanen garuruwan.


Majalisar, don haka, ta bukaci rundunar sojojin Najeriya ta shirya atisaye na musamman don kawar da yan ta’adda da wasu bata gari a yankin na Kainji Lake National Park da garuruwan da ke kewayensa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *