“Najeriya ta koma matsayin na 143 a tsakkiyar wannan shekarar daga matsayi na 146 a matakin zaman lafiya na duniya cikin kasashe 163” – Rahoton zaman lafiya na duniya daga kungiyar Global Peace.

Wani rahoton zaman lafiya na duniya da kungiyar Global Peace kan fitar duk shekara ya nuna yadda Najeriya ta koma matsayin na 143 a tsakkiyar wannan shekarar daga matsayi na 146 a matakin zaman lafiya na duniya cikin kasashe 163.

Wani rahoton zaman lafiya na duniya da kungiyar Global Peace kan fitar duk shekara ya nuna yadda Najeriya ta koma matsayin na 143 a tsakkiyar wannan shekarar daga matsayi na 146 a matakin zaman lafiya na duniya cikin kasashe 163.


Alkaluman na Global Peace ya nuna cewa Iceland ce kasar da ta fi zaman lafiya a duniya sai New Zealand ta 2 kana Ireland ta uku sai Denmark ta hudu sannan Austria ta 5 Portugal ta 6 sai Slovenia ta 7 sannan Singapore ta 8 Japan ta 9 .


A yanzu Najeriya ta matsa da maki 3 idan ta koma ta 143 daga cikinnkasashe 163 masu zaman lafiya aka kwatanta da matakin da ta ke a bara, sai dai ta na kasan kasashe irinsu Mauritania da ke matsayi ta 28 a matakin zaman lafiya a duniya kuma ta 1 a Afrika, sai Ghana matsayin na 40 kana Ganbia na 45 sai Saliyo na 50 da Equatorial Guinea ta 59 sannan Malawi ta 65 sai Senegal na 70, Marocco ta 74 Rwanda 72 Liberia da Gabon na 75 Angola 78 kana Lesotho 100 kana Madagascar da Mozambique da kuma Namibia matsayin na 8 122 da kuma 68.


Sauran kasashen sun kunshi Zambia matsayin ta 56 kana Tunisia ta 85 sai Tanzania ta 86 kana Nijar ta 140 sai Burundi ta 131 da kuma Benin matsayin ta 105, Togo na matsayin ta 102 yayinda Mali ke matsayin ta 150 kana Libya a ta 151 da kuma Burkina Faso a matsayin ta 146 sai Habasha da Sudan matsayin na 149 da kuma 159.


Kasashe mafi kololuwar rashin zaman lafiya kamar yadda alkaluman suka nuna su ne Afghanistan da Yemen da Syria da kuma Rasha kana Sudan ta kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *