Mutum biyu daga cikin maniyyata aikin Hajji sun rasu kafin tashin Jirginsu.

Mahajjata biyu daga yankin ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna, Yakubu Abdulsamad da Haruna Suleiman sun rasa rayuwarsu kafin zuwan ranar tashinsu.

Rahotanni na nunu da cewa mahajjatan sun rasu ne ranar Lahadi da Litinin, kafin zuwan ranar tashin su zuwa ƙasa mai tsarki. Jami’in dake kula da Mahajjatan ƙaramar hukumar, Aminu Surajo, wanda ya sanar da rasuwar su, ya ce tuni aka musu Jana’iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

An gano cewa mamatan biyu na na cikin tawagar jirgin farko da zasu tashi zuwa ƙasar Saudiyya daga jihar Kaduna amma Allah ya yi na shi ikon.

Ana tsammanin kusan mahajjata 2,491 ake sa ran zasu samu damar sauke Farali a Hajjin bana na shekarar 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *