Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai san da zaman dan takarar matakimakin shugaban kasa na wucin gadi da jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar ba.


Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na INEC, Barista Festus Okoye, ya bayyana cewa Dokar Zabe ta 2022 ba ta yi wani tanadi domin daukar abokin takara na wucin gadi ba.


Okoye ya ce, Matsayin dan takarar wucin gadi wani abu ne da aka kirkiro a Najeriya amma kwata-kwata dokar zabe ba ta san da hakan ba,a dan haka dole ne Tunubu ya cigaba da zama da wanda ya mika sunansa a matsayinsa na mataimakinsa.


A ranar 17 ga watan Yuni, 2022 ne wa’adin da INEC ta sanya wa ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 su mika mata sunayen wadanda za su zama mataimakansu ya cika.


Gabanin cikar wa’adin ne Tinubu da takwaransa na jam’iyyar SPD suka gabatar da sunayen mutanen da suka kira ‘abokan takara na wucin gadi’.


Tinubu ya zabi Sakaren Kula da Walwalar Jama’a na Jam’iyyar APC, Kabiru Masari a matsayin abokin takararsa.
Amma wasu masu ruwa da tsaki a APC sun ce Kabiru Masari abokin takara na wucin gadi ne, kafin daga baya Tinubu ya bayyana abokin takararsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.