Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya Nada ‘Dan-Agundi Mukaddashin Manajan Daraktan KSCPC.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya amince da nada Baffa Babba Dan-Agundi a matsayin mukaddashin Manajan Daraktan na Hukumar kula da kayyakin siyarwa na Kano (KSCPC).

Hakan ya bayyana ne a wata takarda da babban sakataran yada labaran gwamna, Abba Anwar ya fitar a ranar Litinin a Kano.

Anwar ya ce nadin ya fara aiki ne tun daga lokacin da Manajan Daraktan ya ajiye aikinsa.

“A matsayinsa na MD rikon kwarya, zai lura da dukkan al’amuran hukumar, daga na aiki har da sauransu, da sa ran daidaita komai yadda ya dace, kafin a nada manaja na dindindin,”

a cewarsa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito yadda aka nada Dan-Agundi a matsayin daraktan hukumar kula da lamurran kan titi na Kano (KAROTA) a baya. NAN ta ruwaito yadda manajan daraktan KSCPC, janar Idris Bello Dambazau (mai ritaya) ya ajiye aikinsa da kansa babu gaira babu dalili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *