Akalla mutane dubu 3 da 478 aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da 2,256 a kasar nan daga watan Disambar 2021 zuwa watan Yunin 2022.

Rahotanni nacewa wasu alkaluma daga cibiyar nazari da binciken lamuran tsaro ta Nigeria Security Tracker, wadda ta tattara jerin hare-haren da suka faru daga watan Disambar bara zuwa yanzu.


Kamar yadda rahoton ya nuna, a watan Disambar 2021 an kashe akalla mutum 342 yayin da aka yi garkuwa da 397 da suka hada da manoma 45 a jihar Nasarawa.


Rahoton ya kuma nuna cewa a watan Janairu an kashe akalla 844, yayin da aka yi garkuwa da wasu 603.
Sanannu daga jerin hare-hare a watan su ne na jihar Zamfara da Neja, inda aka kashe sama da mutum 400 a tsakanin jihohin biyu.


Nigeria Security Tracker ta kuma gano cewa mafi yawan hare-haren da mutanen da aka kashe a Arewacin kasar ne, duk da a Kudancin kasar ana zargin Kungiyar yan Awaren IPOB da aikata kashe kashe.


Amma a Arewaci an fi zargin barayin daji da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Neja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *