Tsohon ministan ma’aikatar kula da Harkokin Neja Delta Godsday Orubebe ya sanar da barin jam’iyyar hamayya ta PDP.

Orubebe ya sanar da ficewar ne a wasikar da ya aike wa Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu.


A cewar Mr Orubebe halin da PDP take ciki a halin yanzu ya nuna cewa jam’iyyar ba ta shirya cin zaben 2023 ba.


Sunan tsohon ministan ya karade shafukan sada zumunta a lokacin zaben 2015, a lokacin da ya kasa ya tsare a zauren bayyana sakamakon zabe, yana ikirarin cewa INEC ba ta shirya yi wa PDP adalci ba a wancan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *