Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta karyata cewa dan takararta Rabiu Musa Kwankwaso zai yi wa Peter Obi na Labour Party mataimaki a zabe mai zuwa.

Sakataren yada labarai na NNPP Dr Agbo Major, ya ce labarin abin kunya gare su kuma babu wani kamshin gaskiya a cikinsa.


Major ya tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP tana tattaunawa kan yiwuwar maja da Labour Party amma har yanzu ba a cimma da wata matsaya ba.


Duk da cewa Kwankwaso bai ambaci cewa shi ko Obi zai zama mataimaki ba, ya ce majar za ta yi tasiri gabannin babban zaben 2023.


Amma, NNPP, cikin sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta na kasa, Dr Agbo Major, ta ce jam’iyyar ta samu labarai cewa Kwankwaso zai iya zama mataimakin Obi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.