Akalla mutane 36 ne aka ruwaito an yi garkuwa da su a wani harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Mazauna kauyukan ne suka bayyana hakan a wata ganawa da jami’an tsaro a wannan rana ta Litinin.


Mazauna yankin sun ce hare-haren da ake kai wa a kai a kai ya shafi rayuwarsu, domin ba za su iya zuwa gonakinsu ba a halin yanzu don gudun kada ‘yan bindiga su kashe su.


Sun kuma ce suna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Kajuru domin ita kadai ce hanyar da za a magance matsalar tsaro.


Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya jagoranci jami’an tsaro zuwa gundumar Kufaina domin samun cikakken bayani game da harin tare da tattaunawa da jama’ar kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *