A kalla 44% na Mutanen Najeriya da suka je taimakawa Ukraine a yakin Rasha sun rasa rayunka su sakamakon yakin.

Ana maganar mutane akalla 38 daga Najeriya da suke taimakawa kasar Ukraine a yakin da ta ke yi da Rasha, suka hallaka zuwa yanzu.

Wani rahoto da Rediyo Faransa ta fitar a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni 2022, ya tabbatar da cewa Najeriya ta yi asarar mutanenta 38 a Ukraine.

Ma’aikatar tsaro na kasar Rasha ta fitar da alkaluma a game da yakin da ake yi da Ukraine, ta ce an samu sojojin hayan Najeriya da aka kashe.

Akwai mutane kusan 85 daga Najeriya da suka yi karfin hali, su ka shiga Ukraine da nufin ba kasar agaji a kan sojojin Vladimir Putin na Rasha.

Daga cikin wadannan sojojin haya, an kashe 38, sannan kuma 35 sun koma inda suka fito. RFI ta ce mutum 12 aka bari yanzu suna cigaba da yakin

Kamar yadda gwamnatin Rasha ta sanar, ta ce makudan kudin da Ukraine ke biyan sojojin hayan, wannan bai hana dakarun Rasha aika su barzahu ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *