Shugaban ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen jihar Kaduna, Ibrahim Ɗalhatu, ya yi Allah waɗai da matakin korar malamai 2,357 a Kaduna bayan faɗuwa jarabawar cancanta.
An ruwaito cewa Ɗalhatu ya ayyana matakin da gwamnatin Kaduna ta ɗauka da ya saɓa wa doka. A wata sanar da hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) ta fitar ta hannun Hauwa Muhammed, ta ce hukumar ta gudanar da jarabawa kan Malamai sama da 30,000 a watan Disamba, 2021.
Tace hukumar ta kori Malaman makarantun Firamare 2,192 ciki har da shugaban ƙungiyar NUT ta ƙasa bisa ƙin zama jarabawar gwaji da gwamnati ta gudanar.
A cewarta, Malamai 165 cikin 27, 662 da suka zauna jarabawar gwajin an kore su saboda gaza cin jarabawan. Wani sashin sanarwan ta ce:
“Biyo bayan matsayar gwamnati na cigaba da gwajin Malamai domin inganta karatu ga yan Kaduna, KADSUBEB ta sake gudanar da jarabawar gwaji a Disamba, 2021. Ba’a buƙatar aikin Malaman da suka ci ƙasa da kashi 40, an sallame su.”
“Malaman da suka ci kashi 75% zuwa sama ne suka tsallake gwajin kuma sun cancanci su halarci horarwa kan shugabanci da harkokin koyarwa a makarantu. Malaman da suka ci tsakanin kaso 40-75% za’a sake basu dama don inganta kwarewar su.”
“Muna tabbatar wa malamai da sauran al’umma cewa zamu cigaba da yin duk abin da zai kawo cigaba da inganta ilimin kananan yara da sauran ɗalibai.”
Da yake martani shugaban NUT, Ibrahim Dalhatu, ya bayyana jarabawan gwajin da kuma korar malamai da cewa sun saɓa wa doka.
“Mun sami umarnin Kotu na hana hukumar gudanar da gwajin, ta yi kunnen uwar shegu da umarnin doka. Mun umarci Malamai ka da su zauna jarabawan saboda mun gano wata maƙarƙashiya ce da aka shirya don korar su.”
“Mun gargaɗi Malamai cewa duk wanda ya zauna jarabawan wacce ta saɓa doka ba zamu kare shi ba, amma wasu suka banzatar da mu suka rubuta saboda tsoro.”
“Bamu ƙi a gudanar da gwajin ba amma abi matakai da ya dace, bai kamata a yi amfani da ita wajen korar ma’aikata ba. Kamata ya yi a yi jarabawan da nufin gano inda malamai ke da rauni, a shirya horarwa don ƙara musu kwarewa.”