Yau Lahadi Jihar Sokoto za ta fara kwasar alhazanta zuwa kasa Mai tsarki .

Babban sakataren hukumar kula da jin dadin alhazai a jihar, Shehu Muhammad Dange, shi ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.


Shehu Muhammad ya ce jihar na da adadin maniyyata 2,404.
Ya ce tuni hukumar ta samar wa alhazai 1,000 biza da kuma kudaden alawus. Ya kara da cewa an yi wa dukkan alhazan jihar allurar rigakafin korona.


Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya nada kakakin majalisar dokokin jihar a matsayin shugaban tawagar alhazan a aikin hajjin na bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *