Rundunar ƴan sandan Najeriya ta damƙe wani matashi a Kano wanda ake zargi da amfani da shafukan bogi a kafafen sada zumunta domin yaudarar jama’a.

Mai magana da yawun ƴan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook inda ya ce sun samu nasarar kama matashin mai suna Musa Lurwanu mai shekara 26 ne bayan tattara bayanan sirri da kuma bin diddiƙin lamarin.


Ya bayyana cewa tun da farko sun samu ƙorafe-ƙorafe ne tun a watan Afrilun bana kan yadda wani ya yi ƙaurin suna a kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da sunayen maza da mata da hotunansu domin buɗe shafuka a Facebook da Twitter da Whatsapp da dai sauransu domin yaudarar mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *