Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Biodun Abayomi Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti.

A daren jiya ne hukumar INEC ta ce Mista Oyebanji ya samu kuri’u 178,057.


Hakan ya sanya jam’iyyar APC ta zamo wadda ta samu kuri’u mafi yawa a zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Yunin shekara ta 2022.


Dan takarar jam’iyyar SDP Olusegun Oni, shi ne ya zo na biyu a zaben inda ya samu kuri’u 82,211.


Sai jam’iyyar PDP wadda ta zo ta uku, inda dan takararta Bisi Kolawole ya samu kuri’u 67,457.


Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar APC ce ta lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar, inda jam’iyyar PDP ta yi nasara a karamar hukuma daya tal.


Magoya bayan jam’iyar APC sun shafe Daren jiya har zuwa wayewar Garin yau suna murna da bukukuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *