Daga gobe litinin , maikatan jihar Zamfara zasu fara hutun mako daya domin karbar katinsu na zabe .

Gwamna Matawalle na Jihar Zamfara ya bada hutun mako daya ga.maikata daga gobe litinin zuwa Jumaa domin samun damar mallakar katin zabe .


Kwamishinan yada Labarai, na jihar Ibrahim Dosara,ne bayyana hakan cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai a Gusau.


Yace daga Ranar Jumaa babu uzuri ga Wanda bai mallaki katinsa na zabe ba a jihar .


Sannan gwamnan jihar Matawalle ya bada umarni ga masu ruwa da tsaki Kan su tabbatar Ma’aikatan da aka bada hutun kwana 5 dominsu , sun mallaki katin Zaben kafin lokaci ya kure.

Leave a Reply

Your email address will not be published.