Kiran ya fito be daga bakin janar Ibrahim Sani mai ritaya, sa’ilin da yake tallafa wa wasu iyaye mata da abin dogaro da kai a unguwar yakasai.
Janar Ibrahim yace Jama’a na cikin matsanancin halin rayuwa da sai an Samar shugabannin na gari da zasu kula da bukatun su.
Janar Ibrahim mai ritaya ya kuma yi nuni da wasu kalubale da kano ke fuskan ta da yakamata masu ruwa da tsaki su bada kulawa.