Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa za a daina amfani da kananzir da icen girki a Najeriya daga shekara ta 2030.

Buhari ya bayyana cewa zuwa lokacin gwamnati za ta sa amfani da gas din girki ya maye gurbin kananzir da icen girki domin rage gurbacewar iska da kuma sauyin yanayi a kasar.


Yace gwamnatin Najeriya na sane da cewar yawan dogaro da makamashi mai fitar da hayaki na jefa kasarnan cikin barazana adaidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin daina amfani dashi a matsayin kashin bayan tattalin arzikinsu.


Shugaba Buhari ya bayyana cewa komawa amfani da gas din girki zai rage gurbacewar iska da kashi 22 cikin 100 a Najeriya zuwa shekara ta 2030, ya kuma taimaka wajen rage sauyin yanayi a fadin duniya.


Ya kara da cewa zuwa lokacin za a yawaita amfani da bas din haya a matsayin babbar hanyar sufuri a Najeriya kuma za a hana kona bolar gona da nufin takaita gurbacewar iska a fadin kasar.


Ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake zantawar da Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, ta bidiyo a ranar Juma’a.


Tun a shekarar 2012 Gwamnatin Tarayya da masu ruwa da tsaki a bangaren mai suka fara aikin samar da dokar hana amfani da kananzir da icen girki da nufin maye gurbinsu da gas din girki.


Shugaban Buhari ya bayyanawa Biden cewar Najeriya tayi sabbin gyare-gyare ga daftarin dokar data gabatarwa taron duniya kan magance sauyin yanayi domin dacewa da zamani.

One Reply to “Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa za a daina amfani da kananzir da icen girki a Najeriya daga shekara ta 2030.

Leave a Reply

Your email address will not be published.