Mu na tattaunawa da su Peter Obi – Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023.

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya zanta da manema labarai a kan shirin 2023. A wasu hira da aka yi da shi a gidajen rediyon BBC Hausa da VOA Hausa, Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida cewa su na ta tattaunawa da bangaren Peter Obi.

Kamar yadda mu ka samu labari a safiyar Asabar, 18 ga watan Yuni 2022, Sanata Rabiu Kwankwaso yana kokarin ganin yadda za a bullowa 2023.

Wani Hadimin tsohon gwamnan na jihar Kano, Saifullahi Muhammad Hassan ya tabbatar da wannan magana a shafinsa na Facebook a daren na Asabar.

A gajeren jawabin da ya fitar, Saifullahi Muhammad Hassan bai yi wani karin-haske ba, sai dai kurum ya tabbatar da rade-radin da ke ta faman yawo a gari.

tattaunawarsa da VOA Hausa, Kwankwaso ya ce tuni jam’iyyar NNPP ta bada sunan abokin takararsa a zaben 2023, amma wanda aka zaba na wucin-gadi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *