Kwankwaso: Na tabbata Zan Yi Nasara, Ba Zan Janye Wa Atiku Ko Tinubu Ba.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya ce ba zai janye wa kowa takararsa ba har da yan takarar manyan jam’iyyun APC da PDP, wato Bola Tinubu da Atiku Abubakar.

Jagoran na Kwankwasiyya ya bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da ya yi da wakilin Jaridar The Punch, Abiodun Sanusi.

Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce tafiyar Kwankwasiya ta bazu dukkan sassan Najeriya kuma ya yi farin cikin ganin an ratabba hannu kan sabuwar dokar zabe don hakan na nufin zai yi wuya a murde zabe kamar yadda aka saba yi a baya.

“Muddin za a yi zabe na adalci, zai yi wahala wani ya doke mu, ina da tabbacin samun nasara kan dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu da na PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023,”

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Yayin da ya ke amsa tambaya kan yiwuwar janye wa Atiku a zaben don kayar da APC, ya ce:

“Ba zan janye wa kowa ba, jam’iyyar mu ta yi fice a dukkan sassan kasar nan, muna da tabbacin za mu ci zabe”.

“Mun zabi yan takarar mu ne kan cancanta da aiki. Yan Najeriya ba za su zabi wani don gwaji ba yanzu, mutane na neman wadanda suka yi aiki a baya. Yan Najeriya na neman wanda zai hada kan al’umma, inganta ilimi, kawo karshen rashin tsaro. Mun dade muna kulawa da al’umma, musamman talakawa, mun yi farin ciki da na samu tikitin takarar shugaban kasa na NNPP.”

Kwankwaso ya ce baya ganin Tinubu da Atiku a matsayin kalubale domin ba shi ne zai kada su ba, talakawan Najeriya ne za su kada su saboda sun yarda da jam’iyyar NNPP.

“Duk da suna na da tambarin jam’iyyar mu ne ke takardar zabe, mutane ne za su fita su kada kuri’a su kayar da su domin sun san banbanci tsakanin ni da sauran yan takarar manyan jam’iyyun, yan Najeriya sun san su, sun san babu wani sabon abu da za su musu, kuma mutanen sun san abin da na yi imani da shi,”

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *