Hukumar yaki da cin hanci ta rashawa ta EFCC ta ce ‘yan Najeriya sun sare da kwarmata bayanai kan wasu masu satar kudin gwamnati Tarayyar, duk da babban kudin lada da ke tattare da yin hakan.

Shugaban hukumar ta EFCC, Abdullahi Bawa, ya shaida hakan lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Kwara, na jihar Ilorin.


Shugaban ya ce akwai bukatar sake jan hankalin mutane da ankarar da su muhimmanci yin haka a kokarin kwato kudaden sata da sake gina tattalin arzikin kasa.


Sai dai hukumar ba ta yi karin haske ko shaida dalilan da suka sa ‘yan Najeriya suka sare da bada bayanan ba.


Tun a shekara ta 2016 gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin kwarmata bayanai da zummar bai wa ma’aikata da ɗaiɗaikun mutane damar fallasa ayyukan cin hanci da rashawa, ita kuma gwamnati ta saka musu da kuɗin lada.


A cewar Ministar Kuɗi ta lokacin, babbar hikimar ɓullo da shirin ita ce taimaka wa yaƙi da rashawa ta hanyar yawaita bankaɗo laifukan da kuma bai wa masu bankaɗowar lada.


Haka zalika a shekara ta 2021, EFCC, ta kaddamar da wata manhaja da zata baiwa ‘yan kasarnan damar daukar hotunan abubuwa ko wuraren da ake aikata laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.