Hukumar hana fasa-kwauri ta kasa ta sanarwa da manema labarai cewar ma’aikatanta sun kama kayan da akayi fasa kaurinsu kuma masu kayan sun biya Naira miliyan 38 cikin wannan watan da ake ciki.

Babban jami’in da ke kula da ofishin hukumar a Jihar Katsina, Dalhatu Chidi-Wada ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a Katsina.


Rahotanni na cewar bude kan iyakar Najeriya da Nijar a garin Jibia ya taimakawa yawancin al’umomin yankin su gudanar da harkokin kasuwancinsu kamar yadda doka ta tanadar.


Dalhatu Chidi-Wada ya ce yawan kayan da ake shigarwa da fitarwa kan iyakar ta Jibia cikin watan daya gabata ya hadarda tan 4,000 na nau’in gas na LNG da tan 1,000 na siminti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *