An bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jam’iyyar (APC) a zaben 2023

Lamarin na zuwa ne yan awanni bayan Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janyewa shugaban majalisar dattawan ba.


Sanata Lawan dai ya yi takarar neman shugaban kasa na jam’iyyar APC sannan awanni kafin fara zaben fidda gwanin sai shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shi a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar.


Sai dai kuma, manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun yi watsi da shawarar maslahar sannan a karshe Bola Ahmed Tinubu ya lashe tikitin a zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.


Da yake ganawa da manema labarai Machina ya jadadda cewa ba zai janye daga tseren kujerar sanatan ba tunda shi ya samu kuri’un deliget a zaben ba tare da hamayya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *