A yaune,ake gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Ekiti.

`Yan takara goma sha shida ne suke fafatawa a zaben.

Duk wanda ya yi nasara a zaɓen zai maye gurbin gwamna mai barin gado Kayode Fayemi na Jam’iyyar APC, wanda a cikin shekarar nan wa’adin mulkinsa zai ƙare.

Tun a watan Janairu ne jam’iyyu suka gudanar da zaɓukan fitar da gwanayensu, kuma sunayen waɗanda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta tantance ne kawai za su kasance a kan ƙuri’ar zaɓen.

A daidai lokacin da ake gudanar da zaɓe a Jihar Ekiti, wasu daga cikin ƴan kasuwa na ci gaba da gudanar da kasuwancinsu kamar yadda suka saba.

Mata ƴan kasuwa sun taru a kasuwar Esa Oke da ke Ado-Ekiti domin gudanar da kasuwancinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *