Ɗan takarar Sanata a Yobe ta Arewa karkashin jam’iyyar APC, Bashir Sheriff Machina, ya ce yana iza zama shugaban majalisar dattawa nan gaba.

A wata hira da jaridar Najeriya ta Leadership ta yi da shi, ɗan takarar ya ce mutane na ta tuntubarsa da sunan ya janyewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, amma hakan ba mai yiwuwa ba ne.


Tana dai ƙasa tana dabo game da makomar siyasar shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmed Lawan, bayan ya rasa takarar shugaban ƙasa a APC da ya nema, wanda Bola Tinubu ya lashe.


Kuma shekarunsa 15 yana rike da kujerar Sanata a Yobe ta Arewa.


A tattaunawarsa da manema labarai, Bashir Machina, ya ce ya fitar da takarda a shafukan sada zumunta wanda ya aikewa jam’iyya, kan tuntubar da aka yi ma sa ko yana nan kan takararsa.


Ya ce shi kuma ya amsa da cewa bai janye ba, kuma yana kan takararsa. Sannan ya ce shi baki da baki Ahmed Lawan bai tuntube shi ba, don haka yana nan kan bakarsa kamar yada jama’a suka zaɓe shi.


Bashir ya kuma ce yana kan bakarsa, kuma yana da tabbacin nasara, saboda manufar takararsa ita ce jagoranci nagari, saboda jama’a su samu wakilci na gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.