‘Yan Najeriya Sun Dena Kazar-kazar Wurin Tona Asirin Masu ‘Sata’ Duk La’ada Mai Tsoka Da Muke Basu – Shugaban EFCC

Mr Abdullahi Bawa, Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ya koka kan yadda yan Najeriya suka dena tona asirin masu tona asirin.

Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta nuna rashin jin dadinta kan yadda yan Najeriya ke nuna halin ko in kula ga tsarin tona asirin masu laifi da Gwamnatin Tarayya ta kaddamar duk da lada da ake biya, rahoton Daily Trust. Shugaban EFCC na kasa, Abdullahi Bawa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin wani taron jin ra’ayin al’umma na kwana guda kan karfafa masu ruwa da tsaki a kan tsarin tona asirin masu laifi da aka yi a Ilorin, Jihar Kwara.

An shirya taron ne da hadin gwiwa da Cibiyar Ilimin Watsa Labarai da Sadarwa, AFRICMIL, da gudunmawar gidauniyar MacArthur.

Yace:

“Manyan kudaden da aka gano karkashin shirin sune $9.8m daga tsohon manajan NNPC, Mr Andrew Yakubu, da $11m daga wani gida a Osborne Towers, Ikoyi Legas”.

“Yadda al’umma suke janye kafa daga shirin abin mamaki ne duba da cewa an biya la’ada mai tsoka ga wadanda suka fara rungumar shirin.”

Bawa, wanda ya samu wakilcin Direktan Sashin Hulda da Al’umma EFCC, Osita Nwajah, ya ce akwai bukatar wayar da kan al’umma su cigaba da bawa hukumomin tsaro bayanai masu amfani”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *