Shugaban jam’iyyar APC Adamu Abdullahi ya bayyana abu daya da zai sa APC su yi nasara a zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar All Progressive Congress APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana yaƙininsa cewa jam’iyya mai mulki zata lashe zaɓen 2023 matuƙar sahihin zaɓen aka gudanar. Adamu ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi bakuncin jakadar Poland a Najeriya, Joanna Tarnawska a ofishinsa ranar Laraba.

Adamu ya ce:

“Tare da ɗumbin goyon bayan da jam’iyyar ke samu daga yan Najeriya miliyan 43m, ba bu ta yadda zata faɗi zaɓen 2023.”

“Jam’iyyar APC ta san abin da zai biyo bayan samun cigaba a Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar Afirka kuma mun shirya sadaukar da kan mu a zaɓen dake tafe kamar yadda muke gani a sauran ƙasashe”.

“Najeriya ƙasa ce mai tasowa a cigaban demokaraɗiyya kuma tana ɗaukar darasi a matakan gudanar da zaɓe, amma APC zata cigaba da yin duk me yuwuwa don demokaraɗiyya ta ƙara samun gindin zama a Najeriya.”

Adamu ya sanar da jakadan Poland ɗin cewa, sakamakon damar da APC ke ba kowa, an samu mace da ta lashe zaɓen takarar gwamnan a jihar arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *