Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace Gwamnatin sa zata ɗauki tsatsauran Mataki dake haifar da Tsoro da Matsalar Tsaro a Najeriya.

Shugaban yayi kira ga Sabbin Jami’ai na Rundunar Ƴan Sandan Najeriya dasu ƙara azama domin cigaba da tsaron Ƙasarnan akan ƴan ta’adda wanda suke so kullum ƴan ƙasa su kasance cikin tsaro.


Dayake jawabi a lokacin bikin yaye Ƴan Sanda na Makantar Horas da Ƴan Sanda ta Wudil dake nan Kano, Shugaba Buhari yace Gwamnatin sa nayin aiki tuƙuru da Tattalin Arzikinta domin ganin ta sanya Rundunar Ƴan Sandan Najeriya “daga cikin jami’an tsaro Masu ƙarfi a faɗin Duniya.


Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa akan Kafafen Yaɗa Labarai mal Garba Shehu ne, ya bayyana hakan.


Da yake bada jawabi akan yaki da Matsalar Tsaro,shugaba Buhari yace Ƴan Boko Haram, da Ƴan IPOB, da Ƴan Bindiga a wasu sassan Ƙasarnan, an rage masu karfi sosai, kumi tuni zaman lafiya ya dawo a wasu garuruwa dake sassan kasarnan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *