Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce binciken ta kawo yanzu ya nuna cewa rahotannin da aka yi ta bayarwa kan sace mutane da dama a Abuja babban birnin kasar a ranar Talata, ba gaskiya ba ne.

Rundunar ta ce wadda ta fara wallafa labarin a Twitter mai suna Amira Sufyan tana hannun jami’ansa cikin yanayi na tsaro, kuma babu gaskiya kan batun sace ta da wasu mutanen.


Labarin ya ja hankali sosai tsakanin ‘yan kasa musamman a Twitter, bayan sakon matashiyar na cewa an saceta tare da wasu mata biyu masu juna biyu kuma ana hanyar daji da su.


Sakon ya yi ikirarin cewa ‘yan bindiga sanye da kakin ‘yan sanda ne suka sace su, har da yara a cikinsu.


Sai dai sanarwar ‘yan sanda na cewa labarin na boge ne, kuma a halin yanzu matashiyar na karkashin kulawarsu a asibitin da ake duba lafiyarta.


Amma sanarwar ba ta bada cikakken bayani ko karin haske kan ainihin abin da ya faru, ko abin da ya kai ga wannan labarin.


Rundunar dai ta ce tana bincike kuma nan gaba kadan za ta sanarwa al’umma sakamakon nazarin nata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.