Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta jaddada cewar ba za’a kara wa’adin da ta baiwa jam’iyyun siyasa ba, na mika sunayen yan takarar kujerar shugaban kasa da mataimakansu.

Sakataren yada labaran shugaban hukumar INEC, Rotimi Oyekanmi, ne bayyana hakan a hirarsa da manema ya bayyana cewa hukumar ba zata kara wa’adi ba.


INEC ta bayyana ranar karshe ga jam’iyyun siyasa na mika mata takaran shugaban kasa da mataimakansu.


Hukumar tace a wannan rana ta Juma’a, 17 ga watan Yuni da misalin karfe 6 na yamma, za’a rufe karbar sunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.