Gwamnatin Jihar Filato ta ce an samu wasu mutum biyu da suka kamu da cutar kyandar Biri a Kananan Hukumomin Shendam da Bassa da ke Jihar.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Nimkong Lar, ne ya tabbatar da hakan a ganawarsa da manema labarai a Jos, babban birnin jihar.


Ya kuma ce wanda aka samu da cutar a Shandam ya warke har an sallame shi daga asibiti, yayin da wanda ya kamu daga Bassa ke ci gaba da karbar magani.


Kazalika, Kwamishinan ya ce Ma’aikatar ta mike tsaye domin wayar da kan mutane ka barkewar annobar kyandar Birin.


Ya kuma ce akwai bukatar al’umma su kula da wanke hannu da tsaftar jikinsu da abinci domin hakan zai taimaka wajen samun kariya daga kamuwa da ita.


A hannu guda kuma, ya shawarci ma’aiktan lafiya a Jihar da su rika amfani da na’u’rorin kare kai wajen kulawa da wadanda suka kamu da cutar domin gudin daukarta.


Kazalika Kwamishinan ya ce al’ummar Jihar su kula da ruwan da suke sha, da wanke kayan marmari da kayan lambu kafin su ci, da kuma daina bahaya a bainar jama’a barkatai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *