Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, ya ayyana sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Rahotanni sun bayyana cewar, Tinubu ya bayyana sunansa ne a matsayin wanda zai tsaya takara tare dashi yayin da wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na jam’iyyu suka mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023 ya kare.


Dan siyasar da aka fitar a matsayin mataimakin shugaban kasar ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina.


Hakazalika, ya taba zama sakataren walwala na jam’iyya mai mulki a zamanin Kwamared Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jamiyyar APC na kasa.


Bayan rasuwar ‘Yar’aduwa a 2010, Masari ya koma jam’iyyar CPC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *